@bbchausa

BBC News Hausa

Nigeria
Rundunar 'yan sandan Najeriya ta dakatar da Abba Kyari daga aikin ɗan sanda sakamakon zargin karɓar cin hanci da 'yan sandan Amurka ke yi masa.

Hukumar Kula da Harkokin 'Yan Sanda ta ɗauki matakin dakatar da Mataimakin Kwamishinan 'Yan Sanda DCP Kyari ne biyo bayan shawarar da Sufeto Janar na 'Yan Sanda Usman Alkali Baba ya bayar.

Mai magana da yawun hukumar, Ikechukwu Ani, ya faɗa cikin wata sanarwa cewa dakatarwar za ta fara aiki ne daga ranar Asabar 31 ga watan Yuli.

"Matakin zai ci gaba da aiki har zuwa lokacin da za a kammala binciken zargin da Hukumar Binciken Manyan Laifuka ta Amurka [FBI] ke yi masa," a cewar sanarwar.

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta dakatar da Abba Kyari daga aikin ɗan sanda sakamakon zargin karɓar cin hanci da 'yan sandan Amurka ke yi masa. Hukumar Kula da Harkokin 'Yan Sanda ta ɗauki matakin dakatar da Mataimakin Kwamishinan 'Yan Sanda DCP Kyari ne biyo bayan shawarar da Sufeto Janar na 'Yan Sanda Usman Alkali Baba ya bayar. Mai magana da yawun hukumar, Ikechukwu Ani, ya faɗa cikin wata sanarwa cewa dakatarwar za ta fara aiki ne daga ranar Asabar 31 ga watan Yuli. "Matakin zai ci gaba da aiki har zuwa lokacin da za a kammala binciken zargin da Hukumar Binciken Manyan Laifuka ta Amurka [FBI] ke yi masa," a cewar sanarwar.

August 01, 2021

Disclaimer

The data provides is not authorized by TikTok. We are not an official partner of TikTok.

Use of materials from the resource is permitted only with a link to our resource.

Copyright © 2024 insiflow.com